Ali Nuhu Dalilai 10 da yasa jarumi yazama abun koyi a masana’antarKannywood | test 2 -->


PROMOTE MUSIC/VIDEO      ADVERTISE ON EL


Shortenlink and get Paid




    Friday, September 29, 2017

    START HERE
  • Ali Nuhu Dalilai 10 da yasa jarumi yazama abun koyi a masana’antarKannywood
  • STOP HERE
    Shortenlink and get Paid
    Hakika masana’antar kannywood ta samu babban abun
    al’fahari kasancewa tare da wannan jarumin a masana’antar.

    Ga wasu dalilai 10 da muke ganin cewa sune abubuwan da
    yasa yan arewa ke farin ciki gannin wannan tauraron wanda
    aka wa lakabi na “sarkin kannywood” a talabijin;

    1. Ya dade yana harkar fina-finai

    Tun shekara 1999 Ali nuhu ya fara fitowa cikin fina-finai kuma
    babban shirin da ya fitar dashi idon jama’a shine “sangaya”.

    2. Banda Kannywood jarumin jakada ne a masana’antar
    Nollywood
    Wannan jarumin ya nuna mana cewa banda haushen hausa ya
    kware wajen yin fina-finai cikin harshen turanci.Ya fito a cikin
    shirin nollywood da dama.

    3. Ya amshi lambar yabo da dama
    Wannan jarumin ya amshi lambobin yabo bila adadi cikin gida
    har da ƙasashen waje.

    4. Shi na kowa ne
    Indai ta yadda abokan hamayen shi na masana’antar zasu
    samu karuwa wannan jarumin yana gaba gaba wajen tabbatar
    da haka kuma sauran jaruman na alfahari kasancewa tare
    dashi.

    5. Yana da ƙwarjini har ƙasashen waje da masana’antu daban
    daban
    Hakika idan muka shiga wasu kasashe zamu ji cewa sunan Ali
    Nuhu yana yaduwa sanadiyar rawan da yake takawa a wajen
    yin fim.

    6. A harkar fim ya nuna cewa na “Uba da ɗane
    Shima dai dan sa Ahmad Ali Nuhu ya fara fitowa a fina-finai
    hausa tun yana dan yaro bayan ya bayyana ma uban shi cewa
    shima a gaskiya yana sha’awar yin fim, ganin cewa faduwa ta
    zo dai dai da zama uban ya mara masa baya amma da
    sharadi na dole sai ya dage wajen koyan ilimi kuma zai dinga
    yin haka idan ya samu hutu daga makaranta.

    7. Da ka ganshi ka gan tambarin Arewa
    Shi dai wannan jarumin baya boye ma jama’a a duk inda ya
    sinci kanshi cewa shi ban dan arewa bane kuma kullum yana
    neman yadda zai yada al’adar yan arewa ga sauran jama’a.

    8. Suma masoyan shi suna farin ciki idan suka ci karo dashi
    Ganin cewa ya shahara a fannin shirya fina-finai jarumin baya
    kyamar tarbar masoyan shi a duk inda ya gamu dasu.

    9. Yana son ƙwallon kafa kuma yana tare da tawagar Nijeriya
    dari bisa dari
    Duk wani wassan kwallo da ya danganci Nijeriya tauraron
    Kannywood yana gaba gaba wajen goyon bayan tawagar kuma
    aboki ne ga yan wassan super eagles.

    10. Ko zamu iya cewa mutu ka raba?
    A yanzu dai wannan jarumin yana da shekaru 43 a duniya
    kuma ya kwashi shekara 19 yana nishatarda mu. Har yanzu
    jarumin yana nuna cewa kamar yanzu ya fara wannan sana’ar
    shirya fina-finai kuma ba alamun gazawa tare dashi.
    Daga nan mu dai muna jinjina ma wannan ƙwararren jarumin
    da ayyukan da yake yi wajen fadakarwa, nishatarwa tare da
    ilmantar da mutanen Arewa.
    Disqus Comments
 


Looking for something? Search below

CHECKOUT THESE HOT SECTIONS ON 9MW

...... ...

...... ...


Pages